Az-Zalzalah

سورة الزلزلة

Sura 99 · Madaniyya · 8 ayoyi

99:1Juzu'i 30 · sh. 599

إِذَا زُلْزِلَتِ الْأَرْضُ زِلْزَالَهَا1

Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
99:2Juzu'i 30 · sh. 599

وَأَخْرَجَتِ الْأَرْضُ أَثْقَالَهَا2

Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
99:3Juzu'i 30 · sh. 599

وَقَالَ الْإِنْسَانُ مَا لَهَا3

Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?"
99:4Juzu'i 30 · sh. 599

يَوْمَئِذٍ تُحَدِّثُ أَخْبَارَهَا4

A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
99:5Juzu'i 30 · sh. 599

بِأَنَّ رَبَّكَ أَوْحَىٰ لَهَا5

cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
99:6Juzu'i 30 · sh. 599

يَوْمَئِذٍ يَصْدُرُ النَّاسُ أَشْتَاتًا لِيُرَوْا أَعْمَالَهُمْ6

A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.
99:7Juzu'i 30 · sh. 599

فَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُ7

To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
99:8Juzu'i 30 · sh. 599

وَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُ8

Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.

Kunna daga farkon sura

Abdullah Al-Mattrod - Az-Zalzalah · Tlawati