Al-Adiyat

سورة العاديات

Sura 100 · Makkiyya · 11 ayoyi

100:1Juzu'i 30 · sh. 599

وَالْعَادِيَاتِ ضَبْحًا1

Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.
100:2Juzu'i 30 · sh. 599

فَالْمُورِيَاتِ قَدْحًا2

Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.
100:3Juzu'i 30 · sh. 599

فَالْمُغِيرَاتِ صُبْحًا3

Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.
100:4Juzu'i 30 · sh. 599

فَأَثَرْنَ بِهِ نَقْعًا4

Sai su motsar da ƙũra game da shi.
100:5Juzu'i 30 · sh. 599

فَوَسَطْنَ بِهِ جَمْعًا5

Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.
100:6Juzu'i 30 · sh. 600

إِنَّ الْإِنْسَانَ لِرَبِّهِ لَكَنُودٌ6

Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.
100:7Juzu'i 30 · sh. 600

وَإِنَّهُ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٌ7

Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.
100:8Juzu'i 30 · sh. 600

وَإِنَّهُ لِحُبِّ الْخَيْرِ لَشَدِيدٌ8

Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.
100:9Juzu'i 30 · sh. 600

۞ أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِي الْقُبُورِ9

Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.
100:10Juzu'i 30 · sh. 600

وَحُصِّلَ مَا فِي الصُّدُورِ10

Aka bayyana abin da ke cikin zukata.
100:11Juzu'i 30 · sh. 600

إِنَّ رَبَّهُمْ بِهِمْ يَوْمَئِذٍ لَخَبِيرٌ11

Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?

Kunna daga farkon sura

Abdullah Al-Mattrod - Al-Adiyat · Tlawati