Al-Waqi'ah

سورة الواقعة

Sura 56 · Makkiyya · 96 ayoyi

56:1Juzu'i 27 · sh. 534

إِذَا وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُ1

Idan mai aukuwa ta auku.
56:2Juzu'i 27 · sh. 534

لَيْسَ لِوَقْعَتِهَا كَاذِبَةٌ2

Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
56:3Juzu'i 27 · sh. 534

خَافِضَةٌ رَافِعَةٌ3

(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
56:4Juzu'i 27 · sh. 534

إِذَا رُجَّتِ الْأَرْضُ رَجًّا4

Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
56:5Juzu'i 27 · sh. 534

وَبُسَّتِ الْجِبَالُ بَسًّا5

Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
56:6Juzu'i 27 · sh. 534

فَكَانَتْ هَبَاءً مُنْبَثًّا6

Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
56:7Juzu'i 27 · sh. 534

وَكُنْتُمْ أَزْوَاجًا ثَلَاثَةً7

Kuma kun kasance nau'i uku.
56:8Juzu'i 27 · sh. 534

فَأَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ8

Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
56:9Juzu'i 27 · sh. 534

وَأَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ9

Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
56:10Juzu'i 27 · sh. 534

وَالسَّابِقُونَ السَّابِقُونَ10

Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
56:11Juzu'i 27 · sh. 534

أُولَٰئِكَ الْمُقَرَّبُونَ11

Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
56:12Juzu'i 27 · sh. 534

فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ12

A ckin Aljannar ni'ima.
56:13Juzu'i 27 · sh. 534

ثُلَّةٌ مِنَ الْأَوَّلِينَ13

Jama'a ne daga mutãnen farko.
56:14Juzu'i 27 · sh. 534

وَقَلِيلٌ مِنَ الْآخِرِينَ14

Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
56:15Juzu'i 27 · sh. 534

عَلَىٰ سُرُرٍ مَوْضُونَةٍ15

(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
56:16Juzu'i 27 · sh. 534

مُتَّكِئِينَ عَلَيْهَا مُتَقَابِلِينَ16

Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
56:17Juzu'i 27 · sh. 535

يَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَانٌ مُخَلَّدُونَ17

Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
56:18Juzu'i 27 · sh. 535

بِأَكْوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأْسٍ مِنْ مَعِينٍ18

Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
56:19Juzu'i 27 · sh. 535

لَا يُصَدَّعُونَ عَنْهَا وَلَا يُنْزِفُونَ19

Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
56:20Juzu'i 27 · sh. 535

وَفَاكِهَةٍ مِمَّا يَتَخَيَّرُونَ20

Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
56:21Juzu'i 27 · sh. 535

وَلَحْمِ طَيْرٍ مِمَّا يَشْتَهُونَ21

Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.
56:22Juzu'i 27 · sh. 535

وَحُورٌ عِينٌ22

Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
56:23Juzu'i 27 · sh. 535

كَأَمْثَالِ اللُّؤْلُؤِ الْمَكْنُونِ23

Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.
56:24Juzu'i 27 · sh. 535

جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ24

A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
56:25Juzu'i 27 · sh. 535

لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا تَأْثِيمًا25

Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
56:26Juzu'i 27 · sh. 535

إِلَّا قِيلًا سَلَامًا سَلَامًا26

Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
56:27Juzu'i 27 · sh. 535

وَأَصْحَابُ الْيَمِينِ مَا أَصْحَابُ الْيَمِينِ27

Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
56:28Juzu'i 27 · sh. 535

فِي سِدْرٍ مَخْضُودٍ28

(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
56:29Juzu'i 27 · sh. 535

وَطَلْحٍ مَنْضُودٍ29

Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.
56:30Juzu'i 27 · sh. 535

وَظِلٍّ مَمْدُودٍ30

Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
56:31Juzu'i 27 · sh. 535

وَمَاءٍ مَسْكُوبٍ31

Da wani ruwa mai gudãna.
56:32Juzu'i 27 · sh. 535

وَفَاكِهَةٍ كَثِيرَةٍ32

Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.
56:33Juzu'i 27 · sh. 535

لَا مَقْطُوعَةٍ وَلَا مَمْنُوعَةٍ33

Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
56:34Juzu'i 27 · sh. 535

وَفُرُشٍ مَرْفُوعَةٍ34

Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
56:35Juzu'i 27 · sh. 535

إِنَّا أَنْشَأْنَاهُنَّ إِنْشَاءً35

Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
56:36Juzu'i 27 · sh. 535

فَجَعَلْنَاهُنَّ أَبْكَارًا36

Sa'an nan Muka sanya su budurwai.
56:37Juzu'i 27 · sh. 535

عُرُبًا أَتْرَابًا37

Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
56:38Juzu'i 27 · sh. 535

لِأَصْحَابِ الْيَمِينِ38

Ga mazõwa dãma.
56:39Juzu'i 27 · sh. 535

ثُلَّةٌ مِنَ الْأَوَّلِينَ39

Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
56:40Juzu'i 27 · sh. 535

وَثُلَّةٌ مِنَ الْآخِرِينَ40

Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
56:41Juzu'i 27 · sh. 535

وَأَصْحَابُ الشِّمَالِ مَا أَصْحَابُ الشِّمَالِ41

Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
56:42Juzu'i 27 · sh. 535

فِي سَمُومٍ وَحَمِيمٍ42

Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
56:43Juzu'i 27 · sh. 535

وَظِلٍّ مِنْ يَحْمُومٍ43

Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
56:44Juzu'i 27 · sh. 535

لَا بَارِدٍ وَلَا كَرِيمٍ44

Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.
56:45Juzu'i 27 · sh. 535

إِنَّهُمْ كَانُوا قَبْلَ ذَٰلِكَ مُتْرَفِينَ45

Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
56:46Juzu'i 27 · sh. 535

وَكَانُوا يُصِرُّونَ عَلَى الْحِنْثِ الْعَظِيمِ46

Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
56:47Juzu'i 27 · sh. 535

وَكَانُوا يَقُولُونَ أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ47

Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"
56:48Juzu'i 27 · sh. 535

أَوَآبَاؤُنَا الْأَوَّلُونَ48

"Shin, kuma da ubanninmu na farko?"
56:49Juzu'i 27 · sh. 535

قُلْ إِنَّ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَ49

Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."
56:50Juzu'i 27 · sh. 535

لَمَجْمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَاتِ يَوْمٍ مَعْلُومٍ50

"Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."
56:51Juzu'i 27 · sh. 536

ثُمَّ إِنَّكُمْ أَيُّهَا الضَّالُّونَ الْمُكَذِّبُونَ51

"Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"
56:52Juzu'i 27 · sh. 536

لَآكِلُونَ مِنْ شَجَرٍ مِنْ زَقُّومٍ52

"Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."
56:53Juzu'i 27 · sh. 536

فَمَالِئُونَ مِنْهَا الْبُطُونَ53

"Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."
56:54Juzu'i 27 · sh. 536

فَشَارِبُونَ عَلَيْهِ مِنَ الْحَمِيمِ54

"Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."
56:55Juzu'i 27 · sh. 536

فَشَارِبُونَ شُرْبَ الْهِيمِ55

"Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."
56:56Juzu'i 27 · sh. 536

هَٰذَا نُزُلُهُمْ يَوْمَ الدِّينِ56

Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
56:57Juzu'i 27 · sh. 536

نَحْنُ خَلَقْنَاكُمْ فَلَوْلَا تُصَدِّقُونَ57

Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
56:58Juzu'i 27 · sh. 536

أَفَرَأَيْتُمْ مَا تُمْنُونَ58

Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
56:59Juzu'i 27 · sh. 536

أَأَنْتُمْ تَخْلُقُونَهُ أَمْ نَحْنُ الْخَالِقُونَ59

Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
56:60Juzu'i 27 · sh. 536

نَحْنُ قَدَّرْنَا بَيْنَكُمُ الْمَوْتَ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ60

Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,
56:61Juzu'i 27 · sh. 536

عَلَىٰ أَنْ نُبَدِّلَ أَمْثَالَكُمْ وَنُنْشِئَكُمْ فِي مَا لَا تَعْلَمُونَ61

A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
56:62Juzu'i 27 · sh. 536

وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ النَّشْأَةَ الْأُولَىٰ فَلَوْلَا تَذَكَّرُونَ62

Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
56:63Juzu'i 27 · sh. 536

أَفَرَأَيْتُمْ مَا تَحْرُثُونَ63

Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
56:64Juzu'i 27 · sh. 536

أَأَنْتُمْ تَزْرَعُونَهُ أَمْ نَحْنُ الزَّارِعُونَ64

Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
56:65Juzu'i 27 · sh. 536

لَوْ نَشَاءُ لَجَعَلْنَاهُ حُطَامًا فَظَلْتُمْ تَفَكَّهُونَ65

Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
56:66Juzu'i 27 · sh. 536

إِنَّا لَمُغْرَمُونَ66

(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"
56:67Juzu'i 27 · sh. 536

بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ67

"Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"
56:68Juzu'i 27 · sh. 536

أَفَرَأَيْتُمُ الْمَاءَ الَّذِي تَشْرَبُونَ68

Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
56:69Juzu'i 27 · sh. 536

أَأَنْتُمْ أَنْزَلْتُمُوهُ مِنَ الْمُزْنِ أَمْ نَحْنُ الْمُنْزِلُونَ69

Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
56:70Juzu'i 27 · sh. 536

لَوْ نَشَاءُ جَعَلْنَاهُ أُجَاجًا فَلَوْلَا تَشْكُرُونَ70

Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
56:71Juzu'i 27 · sh. 536

أَفَرَأَيْتُمُ النَّارَ الَّتِي تُورُونَ71

Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
56:72Juzu'i 27 · sh. 536

أَأَنْتُمْ أَنْشَأْتُمْ شَجَرَتَهَا أَمْ نَحْنُ الْمُنْشِئُونَ72

Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
56:73Juzu'i 27 · sh. 536

نَحْنُ جَعَلْنَاهَا تَذْكِرَةً وَمَتَاعًا لِلْمُقْوِينَ73

Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
56:74Juzu'i 27 · sh. 536

فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ74

Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
56:75Juzu'i 27 · sh. 536

۞ فَلَا أُقْسِمُ بِمَوَاقِعِ النُّجُومِ75

To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
56:76Juzu'i 27 · sh. 536

وَإِنَّهُ لَقَسَمٌ لَوْ تَعْلَمُونَ عَظِيمٌ76

Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
56:77Juzu'i 27 · sh. 537

إِنَّهُ لَقُرْآنٌ كَرِيمٌ77

Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
56:78Juzu'i 27 · sh. 537

فِي كِتَابٍ مَكْنُونٍ78

A cikin wani littafi tsararre.
56:80Juzu'i 27 · sh. 537

تَنْزِيلٌ مِنْ رَبِّ الْعَالَمِينَ80

Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
56:81Juzu'i 27 · sh. 537

أَفَبِهَٰذَا الْحَدِيثِ أَنْتُمْ مُدْهِنُونَ81

Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
56:82Juzu'i 27 · sh. 537

وَتَجْعَلُونَ رِزْقَكُمْ أَنَّكُمْ تُكَذِّبُونَ82

Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
56:83Juzu'i 27 · sh. 537

فَلَوْلَا إِذَا بَلَغَتِ الْحُلْقُومَ83

To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
56:84Juzu'i 27 · sh. 537

وَأَنْتُمْ حِينَئِذٍ تَنْظُرُونَ84

Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
56:85Juzu'i 27 · sh. 537

وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنْكُمْ وَلَٰكِنْ لَا تُبْصِرُونَ85

Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
56:86Juzu'i 27 · sh. 537

فَلَوْلَا إِنْ كُنْتُمْ غَيْرَ مَدِينِينَ86

To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
56:87Juzu'i 27 · sh. 537

تَرْجِعُونَهَا إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ87

Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.
56:88Juzu'i 27 · sh. 537

فَأَمَّا إِنْ كَانَ مِنَ الْمُقَرَّبِينَ88

To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
56:89Juzu'i 27 · sh. 537

فَرَوْحٌ وَرَيْحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍ89

Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
56:90Juzu'i 27 · sh. 537

وَأَمَّا إِنْ كَانَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِ90

Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
56:91Juzu'i 27 · sh. 537

فَسَلَامٌ لَكَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِ91

Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
56:92Juzu'i 27 · sh. 537

وَأَمَّا إِنْ كَانَ مِنَ الْمُكَذِّبِينَ الضَّالِّينَ92

Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
56:93Juzu'i 27 · sh. 537

فَنُزُلٌ مِنْ حَمِيمٍ93

Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
56:94Juzu'i 27 · sh. 537

وَتَصْلِيَةُ جَحِيمٍ94

Da ƙõnuwa da Jahĩm,
56:95Juzu'i 27 · sh. 537

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ الْيَقِينِ95

Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
56:96Juzu'i 27 · sh. 537

فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ96

Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.

Kunna daga farkon sura

Fares Abbad - Al-Waqi'ah · Tlawati