Al-Ghashiyah

سورة الغاشية

Sura 88 · Makkiyya · 26 ayoyi

88:1Juzu'i 30 · sh. 592

هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ1

Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
88:2Juzu'i 30 · sh. 592

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ خَاشِعَةٌ2

Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
88:3Juzu'i 30 · sh. 592

عَامِلَةٌ نَاصِبَةٌ3

Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
88:4Juzu'i 30 · sh. 592

تَصْلَىٰ نَارًا حَامِيَةً4

Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
88:5Juzu'i 30 · sh. 592

تُسْقَىٰ مِنْ عَيْنٍ آنِيَةٍ5

Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
88:6Juzu'i 30 · sh. 592

لَيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِنْ ضَرِيعٍ6

Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
88:7Juzu'i 30 · sh. 592

لَا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِي مِنْ جُوعٍ7

Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
88:8Juzu'i 30 · sh. 592

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَاعِمَةٌ8

Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
88:9Juzu'i 30 · sh. 592

لِسَعْيِهَا رَاضِيَةٌ9

Game da aikinsu, masu yarda ne.
88:10Juzu'i 30 · sh. 592

فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ10

(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
88:11Juzu'i 30 · sh. 592

لَا تَسْمَعُ فِيهَا لَاغِيَةً11

Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
88:12Juzu'i 30 · sh. 592

فِيهَا عَيْنٌ جَارِيَةٌ12

A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
88:13Juzu'i 30 · sh. 592

فِيهَا سُرُرٌ مَرْفُوعَةٌ13

A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
88:14Juzu'i 30 · sh. 592

وَأَكْوَابٌ مَوْضُوعَةٌ14

Da kõfuna ar'aje.
88:15Juzu'i 30 · sh. 592

وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌ15

Da filõli jẽre,
88:16Juzu'i 30 · sh. 592

وَزَرَابِيُّ مَبْثُوثَةٌ16

Da katifu shimfiɗe.
88:17Juzu'i 30 · sh. 592

أَفَلَا يَنْظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ17

Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
88:18Juzu'i 30 · sh. 592

وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ18

Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
88:19Juzu'i 30 · sh. 592

وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ19

Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
88:20Juzu'i 30 · sh. 592

وَإِلَى الْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ20

Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
88:21Juzu'i 30 · sh. 592

فَذَكِّرْ إِنَّمَا أَنْتَ مُذَكِّرٌ21

sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
88:22Juzu'i 30 · sh. 592

لَسْتَ عَلَيْهِمْ بِمُصَيْطِرٍ22

Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
88:23Juzu'i 30 · sh. 593

إِلَّا مَنْ تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ23

Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
88:24Juzu'i 30 · sh. 593

فَيُعَذِّبُهُ اللَّهُ الْعَذَابَ الْأَكْبَرَ24

To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
88:25Juzu'i 30 · sh. 593

إِنَّ إِلَيْنَا إِيَابَهُمْ25

Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
88:26Juzu'i 30 · sh. 593

ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُمْ26

Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.

Kunna daga farkon sura