At-Takwir

سورة التكوير

Sura 81 · Makkiyya · 29 ayoyi

81:1Juzu'i 30 · sh. 586

إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ1

Idan rãna aka shafe haskenta
81:2Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا النُّجُومُ انْكَدَرَتْ2

Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
81:3Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْ3

Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
81:4Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْ4

Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
81:5Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْ5

Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
81:6Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْ6

Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
81:7Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ7

Kuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu.
81:8Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا الْمَوْءُودَةُ سُئِلَتْ8

Kuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta.
81:9Juzu'i 30 · sh. 586

بِأَيِّ ذَنْبٍ قُتِلَتْ9

"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
81:10Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْ10

Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
81:11Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا السَّمَاءُ كُشِطَتْ11

Kuma idan sama aka fẽɗe ta.
81:12Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْ12

Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
81:13Juzu'i 30 · sh. 586

وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ13

Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
81:14Juzu'i 30 · sh. 586

عَلِمَتْ نَفْسٌ مَا أَحْضَرَتْ14

Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
81:15Juzu'i 30 · sh. 586

فَلَا أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِ15

To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba.
81:16Juzu'i 30 · sh. 586

الْجَوَارِ الْكُنَّسِ16

Mãsu gudu suna ɓũya.
81:17Juzu'i 30 · sh. 586

وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ17

Da dare idan ya bãyar da bãya.
81:18Juzu'i 30 · sh. 586

وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ18

Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
81:19Juzu'i 30 · sh. 586

إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ19

Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
81:20Juzu'i 30 · sh. 586

ذِي قُوَّةٍ عِنْدَ ذِي الْعَرْشِ مَكِينٍ20

Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
81:21Juzu'i 30 · sh. 586

مُطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ21

Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
81:22Juzu'i 30 · sh. 586

وَمَا صَاحِبُكُمْ بِمَجْنُونٍ22

Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
81:23Juzu'i 30 · sh. 586

وَلَقَدْ رَآهُ بِالْأُفُقِ الْمُبِينِ23

Kuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani.
81:24Juzu'i 30 · sh. 586

وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِينٍ24

Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne.
81:25Juzu'i 30 · sh. 586

وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَانٍ رَجِيمٍ25

Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
81:26Juzu'i 30 · sh. 586

فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ26

Shin, a inã zã ku tafi?
81:27Juzu'i 30 · sh. 586

إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِلْعَالَمِينَ27

Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
81:28Juzu'i 30 · sh. 586

لِمَنْ شَاءَ مِنْكُمْ أَنْ يَسْتَقِيمَ28

Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
81:29Juzu'i 30 · sh. 586

وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَنْ يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ29

Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.

Kunna daga farkon sura